Najeriya

Ambaliya ta kashe mutane 54 a Kano,ta kuma rusa gidaje 30.356

Wasu yankuna da aka fuskanci ambaliya
Wasu yankuna da aka fuskanci ambaliya Seyllou / AFP

Hukumar agajin gaggawa ta Jihar Kano dake Najeriya tace mutane 54 suka mutu sakamakon ambaliyar da aka samu bana, yayin da gidaje 30,356 suka rushe.

Talla

Sakataren hukumar Dr Saleh Jili yace wadannan alkaluma sun fito ne daga daukacin kananan hukumomin Jihar 44 daga watan Yuni zuwa watan Oktoba, yayin da mutane 81 suka samu raunuka.

Yayin da yake tilawar matsalolin da suka fuskanta bana, Sakataren yace an samu gobara sau 2,177, bayan ambaliyar da ta lalata gonaki 9,127, abinda ya sa gwamnatin jihar ta kai dauki ga mutanen da matsalar ta ritsa da su wajen basu kayan ginin da suka hada da siminti da kwanon rufi da bargo da katifa da kuma kayayyakin ayyukan gida.

Ambaliyar ruwa ta zama ruwan dare gama duniya a Najeriya, inda a wannan shekarar matsalar ta shafi kusan kowacce Jiha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI