Najeriya

Masu zanga-zanga sun rufe babbar hanyar Abuja

Wasu daga cikin masu zanga-zanga dangane da rusa rundunar Sars
Wasu daga cikin masu zanga-zanga dangane da rusa rundunar Sars REUTERS/Temilade Adelaja

Masu zanga zangar adawa da cin zarafin Yan Sanda a Najeriya yau sun tare babbar hanyar dake Abuja wadda ke kai mutane rashar jiragen saman Nanmdi Azikiwe, kwanaki bayan gwamnati ta amince da bukatun sun a rusa rundunar SARS dake yaki da Yan fashi da da makami.

Talla

Masu zanga zangar wadanda akasarin su matasa ne sun tattaki zuwa babbar kofar shiga birnin dauke da rubuce rubuce domin nunawa duniya halin da ake ciki a kasar.

Haramta zanga zangar da ministan Abuja yayi bai hana su sake gangami ba, inda suka ci gaba da bayyana korafin su da bukatar ganin an hukunta jami’an da ake zargin sun aikata laifi a tsohuwar rundunar ta SARS.

A jihar Lagos ma masu zanga zangar sun cigaba da gudanar da gangamin su a sassan birnin da suka hada da hanyar Lekki da unguwar Maryland inda suka jefa matafiya cikin halin kunci, yayin da jami’an Yan Sanda suka janye daga tituna.

Mazauna birnin da dama sun shaidawa RFI Hausa irin ukubar da suka sha dangane da yadda zanga zangar ta hana harkokin yau da kullum, yayin da bata gari ke amfani da ita suna kai wa mutane hari suna kuma fasa shaguna.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matasa daga Yankin Arewacin Najeriya suma suka fara gudanar da tasu zanga zangar inda suke bukatar ganin an inganta tsaro domin kawo karshen kashe kashen dake gudana a sassan kasar.

Tuni Gwamnonin Arewacin Najeriya suka fito suka nuna rashin amincewar su da rusa rundunar SARS kamar yadda shugaban su Gwamnan Plateau Simon Lalong ya bayyana bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.