Cote d'Ivoire

'Yan adawa na shirin kaurace wa zaben Ivory Coast

‘Yan adawa a Ivory Coast sun bukaci magoya bayansu da su kaurace wa zaben shugabancin kasar da ke tafe a ranar 31 ga watan Oktoban da muke ciki.

Shugaba Alassane Ouattara mai neman wa'adi na uku, abin da ya fusata masu zanga-zangar.
Shugaba Alassane Ouattara mai neman wa'adi na uku, abin da ya fusata masu zanga-zangar. SIA KAMBOU/AFP
Talla

Gamayyar ‘yan adawar sun dauki matakin ne don ci gaba da nuna bacin rai da shirin shugaba mai ci Alassan Ouattara na neman wa’adi na 3, bayan karewar wa'adinsa na biyu da kundin tsarin mulki ya ba shi dama.

Wannan ta sanya a ciki da wajen Ivory Coast ake fargabar barkewar kazamin rikicin siyasa, irin wanda aka gani a shekarar 2010 zuwa 2011, lokacin da rayukan mutane akalla dubu 3000 suka salwanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI