Tanzania

An dakile gobarar dake cin dajin tsaunin Kilimajaro a Tanzania

Tsaunin Kilimandjaro en Tanzanie.
Tsaunin Kilimandjaro en Tanzanie. Getty Images

A Tanzaniya, Yanzu haka dai an shawo kan gobarar dajin da ta tashi tun ranar 11 ga wanan wata na octoba da muke ciki a dajin dake kewaye da tsaunin Kilimandjaro, mafi tsawon a nahiyar Amrika, bayan da ta kone daji mai fadin muraba’in kilo mita 95 km2 ba tare da ta haddasa wata hasarar rayuka ba, kamar yadda hukumar dake kula da gandun dajin kasar ta Tanapa ta sanar

Talla

Tsaunin dake yankin arewa maso gabashin Tanzaniya, da ke kusa da kan iyaka da kasar Kenya, ya kasance tsauni mai tsawon mita dubu 5.895 daga kasa zuwa sama, wanda kuma ke samun ziyarar masu yawon buda ido, da kuma yan hawan tsauni daga ko wace kusurwa ta duniya.

Kakakin ma’aikatar gandun dajin ta Tanapa, Pascal Shelutete, ya ce, an shawo kan gobarar da ta share kusan mako guda tana ci sai dai bata haddasa wata hasar ta rai ko raunata mutane ba, inda yak ara da cewa, yanzu masu ziyarar buda ido da yan hawan tsauni na iya ci gaba da ziyarartar tsaunin na Kilimanjaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.