Cote d'Ivoire

Fada ya barke a tsakanin yan adawa da na shugaban kasar Cote Ivoire

zanga zangar masu kin jinin sake tsayawa takarar shugabancin kasa karo na uku ga Allasan watara
zanga zangar masu kin jinin sake tsayawa takarar shugabancin kasa karo na uku ga Allasan watara SIA KAMBOU/AFP

A kasar Cote Ivoire ana ci gaba da samun tashe tashen hankulla tsakanin kabilu, al’amariun da ya yi sanadiyar jikkata mutane da dama a garin Bongouanou, mai tazarar kilo mita 150 a arewacin 'Abidjan, cibiyar gwamnatin kasar.Yankin da ke zama tingar zabe ga dan takara shugabancin kasar haka kuma tsohon fira ministan Laurent Gbagbo, cewa da Pascal Affi N'Guessan, da gidansa ke cikin gidajen da aka kona a sabon rikicin, kamar yadda majiyoyin a garin suka sanar da AFP.

Talla

Wannan tashin hankali ya barke ne, a dai dai wannan lokacin da a ranar alhamis da ta gabata, jam’iyun adawa suka bayyana aniyarsu ta kauracewa zabukan kasar, tare da kiran magoya bayansu, da su hana gudanar da zaben shugabancin kasar da ake shirin yi a ranar 31 ga wannan wata na October.

Yan adawar sun kuma bukaci sake fasalta hukumar zaben kasar CENI, da kuma kotun faslta kundin tsarin mulki, da suka zarga da zama yan amshin shatar gwamnatin mai ci.

Mazauna unguwar Agnikro kabilar yanki Bongouanou da kuma yan anguwar Dioulabougou ta yan kabilar dioula dake arewacin kasar, da mafi akasarinsu magoya bayan shugaban kasar mai barin gado Allassan Ouattara ne, sun kuma ba hamuta iska ne da kulake da kuma adduna, kamar yadda shaidun gani da ido da dama da aka yi fira dasu ta wayar telefon suka sanar da AFP. Inda suka ce gidaje da shaguna da dama kuma sun ci wuta a halin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.