Najeriya

An gano dalibai kusan 200 da suka kamu da cutar Corona a Lagos

wasu dalibai a Burkina faso sanye da takunkumin hana kamuwa da  Covid-19
wasu dalibai a Burkina faso sanye da takunkumin hana kamuwa da Covid-19 OLYMPIA DE MAISMONT / AFP

Gwamnatin Jihar Lagos a Najeriya ta ce, dalibai da ma’aikatan wata makaranta a Jihar su 181 sun kamu da cutar korona, bayan sake bude makarantun da aka yi a wannan mako domin cigaba da karatu.

Talla

Kwamishinan Lafiyar Jihar Farfesa Akin Abayomi ya ce, binciken da aka gudanar, bayan da wata daliba yar aji 1 a babbar Sakandare dake unguwar Lekki ta kamu da rashin lafiya, an gano tarin mutane da cutar ta harba.

Abayomi ya ce sun dauki Karin matakai wajen ganin sun dakile yaduwar cutar, da suka hada da killace daukacin daliban da sauran ma’aikatan makarantar domin kula da su baki daya, yayin da aka shaidawa iyayen su.

Jihar Lagos dai ke sahun gaba wajen yawan mutanen da suka kamu da cutar korona a Najeriya, inda take dauke da yawan mutanen dake fama da cutar 20,433, yayin da 204 daga cikin su sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.