Najeriya

Najeriya ta nemi gafarar masu zanga zanga

mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da shugaban rundunar yan sandan kasar, Mohammed Adamu
mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da shugaban rundunar yan sandan kasar, Mohammed Adamu RFI/Ahmed Abba

Gwamnatin Najeriya ta nemi gafarar masu zanga zangar adawa da cin zarafin da ake zargin jama’a da ake zargin Yan Sandan kasar da yi, inda ta bukace su da suyi mata afuwa saboda gazawarta wajen daukar matakan da suka dace tun da wuri wajen shawo kan korafe korafen da suka gabatar.

Talla

Mataimakin shugaban kasar ta Najeriya Yemi Osinbajo, ya gabatar da neman afuwar, a wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, inda ya bayyana cewa, gwamnati na daukar matakan da suka dace, da kuma za su taimaka wajen yi wa ayyukan Yan Sanda, kula da inganta rayuwarsu tare da batun basu horo garambawul domin sake inganta yanayin aikin yan sandan.

Osinbajo yayi alkawarin cewa, babu wani daga cikin jami’an tsohuwar rundunar SARS da zai taka rawa cikin sabuwar rundunar da aka kafa ta SWAT domin ganin an kakkabe hannayen su baki daya.

Mataimakin shugaban kasar ya ce taron Majalisar tattalin arzikin da ya jagoranta, ya amince da kafa kwamitin shari’a da zai yi nazarin korafe korafen da jama’a ke da shi kan tsohuwar rundunar da zummar yin gyara.

A cikin sakon da ya gabatar, Osinbajo ya ce ‘Ya ku Yan Najeriya, mun san cewa, da yawa daga cikin ku sun harzuka, kuma mun yarda da haka. Ya dace mu dauki matakin gaggawa, saboda haka, ku yafe mu.’

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.