Guinea

Al'ummar Guinea na zaben shugaban kasa

Shugaban kasar Guinea Alpha Conde a birnin Conakry
Shugaban kasar Guinea Alpha Conde a birnin Conakry AFP

Al’ummmar Guinea na kada kuri’unsu a zaben shugabancin kasar, bayan zanga-zangar adawa ta watanni da shugaba Alpha Conde ya fuskanta daga dubban ‘yan adawa.

Talla

Kusan mutane miliyan 5 a kasar ta Guinea ake sa ran za su kada kuri’un nasu, a zaben da za a fafata tsakanin shugaba mai ci Alpha Conde da wasu ‘yan takarar 11, wanda tsohon fira ministan kasar Cellou Dalein Diallo ya fi fice a cikinsu.

Shugaba Conde mai shekaru 82 na neman wa’adi na uku, sakamakon nasarar da ya samu ta yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima bayan zaben raba gardamar da ya shirya a watan Maris na wannan shekara, zaben da ‘yan dawa suka kauracewa.

Nasarar gyara kundin tsarin mulkin na Guinea ya baiwa shugaban mai ci damar sake jagorantar kasar na tsawon wasu shekaru 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.