Najeriya

Babu hannu na cikin masu daukar nauyin zanga zanga - Tinubu

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da jagoran APC Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da jagoran APC Bola Ahmed Tinubu Nigeria Presidency/Handout via Reuters

Tsohon Gwamnan Jihar Lagos dake Najeriya kuma jagoran Jam’iyyar APC mai mulkin kasar, Bola Ahmed Tinubu yace babu hannun sa cikin masu daukar nauyin zanga zangar da ake cigaba da gudanarwa a kasar domin adawa da cin zarafin Yan Sanda.

Talla

Sanarwar da kakakin sa Tunde Rahman ya rabawa manema labarai tayi watsi da zargin cewar, tsohon Gwamnan na da hannu wajen goyan bayan zanga zangar da ta shafi tattalin arzikin Lagos da kuma haifar da matsaloli a wasu jihohin kasar.

Rahman yace ya zama wajibi a bayyana gaskiya yadda take domin watsi da labarin kanzon kurege da ake amfani da shi domin batawa jagoran Jam’iyyar APC suna.

Sanarwar tace babu yadda za’ayi Tinubu ya dauki nauyin irin wannan zanga zangar wadda ta rufe daya daga cikin hanyoyin shiga birnin Lagos da Jihar ke samun kudaden shiga, yayin da kuma masu zanga zangar ke cacakar sa.

Rahman yace duk da yake Bola Tinubu ya amince cewar Yan Najeriya na da hurumi da ‘yancin bayyana ra’ayoyin su da gudanar da tarurruka da kuma zanga zanga idan bukatar hakan ta taso, amma shi yafi fifita amfani da hanyar lumana domin bayyana ra’ayoyi da kuma bukatu.

Jami’in yada labaran yace masu zanga zangar sun riga sun gabatar da bukatun su wanda gwamnati ke nazari akai, kuma kamar kowanne dan Najeriya shima baya jin dadi dangane yadda aka dauki dogon lokaci ba’a shawo kan wannan matsala ta rundunar SARS akan mutanen da basu ji basu gani ba, kuma ya dace soke rundunar kamar yadda aka bukata.

Mai magana da yawun tsohon Gwamnan yace fatar Tinubu itace matasa masu zanga zangar da su jira domin tattaunawa da kuma fara aiwatar da sauye sauye daga bangaen gwamnati, yayin da yake watsi da masu danganta shi da daukar nauyin ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.