Ivory Coast

An kone gidan jagoran 'yan adawa a Ivory Coast

Rikicin siyasa ya barke a garin Bangouanou na kasar Ivory Coast
Rikicin siyasa ya barke a garin Bangouanou na kasar Ivory Coast UrduPoint.com

Rikicin siyasa ya barke a Ivory Coast, yayin da ya rage makwanni 2 a gudanar da zaben shugabancin kasar, abinda ya haifar da jikkatar daruruwan mutane.

Talla

Rahotanni sun ce tun a ranar Juma’a rikicin ya barke a garin Bangouanou yankin da fitaccen dan takara mai kalubalantar shugaba mai ci Alassan Ouattara ke da rinjaye, wato jagoran ‘yan adawa kuma tsohon fira ministan kasar Pascal Affi N’Guessan, wanda kuma aka kone gidansa a rikicin.

Tuni dai bangaren ‘yan adawar ya dora alhakin tayar da rikicin kan gwamnati, wadda suka zarga da hayar ‘yan tada zaune tsaye daga birnin Abdijan.

A baya bayan nan 'yan adawa a kasar ta Ivory Coast suka bukaci magoya bayansu da su kaurace wa zaben shugabancin kasar da ke tafe a ranar 31 ga watan Oktoban da muke ciki.

Gamayyar ‘yan adawar sun dauki matakin ne don ci gaba da nuna bacin rai da shirin shugaba mai ci Alassan Ouattara na neman wa’adi na 3, bayan karewar wa'adinsa na biyu da kundin tsarin mulki ya ba shi dama.

Wannan ta sanya a ciki da wajen Ivory Coast ake fargabar barkewar kazamin rikicin siyasa, irin wanda aka gani a shekarar 2010 zuwa 2011, lokacin da rayukan mutane akalla dubu 3000 suka salwanta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.