Najeriya

Atiku ya bayyana rashin dacewar amfani da karfi a kan masu zanga-zanga a Najeriya

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya.
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya. AFP

Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana kaduwar sa da rasa rayukan da aka samu wajen zanga zangar lumana da masu adawa kan cin zarafin da jami’an 'yan sanda ke yi wa fararen hula, wanda yace wasu bata gari sun mamaye.

Talla

A sakon da ya aike ta shafin sa na Facebook, Abubakar ya bukaci gwamnatin Muhammadu Buhari da kar ta amince da shawarar amfani da karfi wajen murkushe masu zanga zangar.

Tsohon mataimakin shugaban ya bayyana masu zanga zangar a matsayin masu hankali dake da aniya mai kyau ga kasa, inda yake cewa yanzu lokaci ne na amincewa da kuma aiwatar da bukatun su.

Abubakar ya ce lokacin da gwamnati ta nunawa 'yan kasa ta damu da su, a lokacin su kuma suke nuna mata kauna, inda ya bukaci shugaban kasa da ya yi wa jama’ar kasa jawabi, musamman  matasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.