Guinea

Hankula sun tashi a Guinea bayan zaben shugaban kasa

Shugaban Guinea Konakry Alpha Conde
Shugaban Guinea Konakry Alpha Conde REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Har yanzu ana ci gaba da zaman fargaba a Guinea bayan an shafe daren jiya ana rikici, biyo bayan ikirarin nasara a zaben shugaban kasar da jagoran ‘yan adawa ya yi.

Talla

Jagoran ‘yan adawa, Cellou Dalein Diallo yana takara ne da shugaba mai ci, Alpha Conde, wanda ke neman wa ‘adi na 3, bayan kwaskwarimar da ya yi wa kundin tsarin mulkin, lamarin da ya janyo cece kuce daga ciki da wajen kasar.

A Litinin dinnan ne Cellou Diallo ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben na 18 ga watan Oktoba, ba tare da ya jira hukumnar da ke da alhakin gudanar da zaben ta yi haka ba, inda ya yi kira ga aal’ummar kasar da su fito su ba dimokaradiyya kariya.

Amma bangaren Conde sun yi watsi da ikirarin nasarar, da ma murnanr wannan nasarar da magoya bayan jagoran ‘yan adawan ke yi, daga nan ne fa tarzoma ta tashi a babban birnin kasar Conakry, inda aka yi ta dauki da dadi da jami’an tsaro.

Diallo, mai shekaru 68, ya wallafa a shafinsa na Tweeter a daren Litin cewa jami’an tsaro sun bude wut a kan taron jama’a, abin da ya yi sanadin mutuwar wasu samari 3, da dama kuma suka jikkata, yana mai daura alhakin barnar a kan shugaba Conde.

Gwamnatin Guinea dai bata tabbatar da batun asarar rai ba, amma kamfanin dillancin labaran Faransa ya tabbatar da jin karar harbe harbe a wajen birnin Conakry, da kuma mutane 3 da suka samu rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.