Hukumar zaben Ghana ta hana 'yan takara 5 tsayawa a zaben shugaban kasar mai zuwa

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo. Paul Marotta/Getty Images

Hukumar zabe a kasar Ghana ta soke takarar mutane 5 dake neman tsayawa a zaben shugaban kasar  mai zuwa sakamakon gabatar da takardun bogi.

Talla

‘Yan takarar da abin ya shafa sun hada da Kofi Koranteng, dan takarar Indifenda da Marricke Kofi Gane shima daga Indifenda da Akwasi Odike na UPP da Kwasi Busumburu na PAP da Agyenim Boateng na UFP

Hukumar ta kuma ce ta mika sunayen wadannan Yan takara ga rundunar Yan Sanda domin gurfanar da su a gaban shari’a, yayin da zata mayar musu da kudaden takarar da suka gabatar na Cedi 100,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.