Burundi

Kotu a Burundi ta yanke wa tsohon shugaban kasar daurin rai da rai

Shugaban Burundi, Evariste Ndayishimiye.
Shugaban Burundi, Evariste Ndayishimiye. AFP Photos/Tchandrou Nitanga

Wata Kotu ta yanke wa tsohon shugaban kasar Burundi Pierre Buyoya hukuncin daurin rai da rai saboda samun sa da laifin kashe wanda ya gada Melchior Ndadaye lokacin da ya jagoranci juyin mulkin da ya hallaka shi a shekarar 1993.

Talla

Kotun ta gabatar da hukuncin ne a bayan idan Buyoya wanda yanzu haka yake aiki a matsayin Jakada na musamman na kungiyar kasashen Afirka a Mali.

Juyin mulkin na shekarar 1993 ya jefa kasar cikin yakin basasan da ya kaiga rasa dimbin rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.