Najeriya-Lagos

Najeriya: Lagos ta ayyana dokar hana zirga-zirga saboda tsanantar zanga-zanga

Masu zanga zangar kawo karshen cin zalin 'yan sanda a Legas.
Masu zanga zangar kawo karshen cin zalin 'yan sanda a Legas. REUTERS/Temilade Adelaja

Gwamnatin Jihar Legas dake Najeriya ta ayyana dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 biyo bayan tarzomar da ta tashi a sassan jihar sakamakon zanga zangar neman kawo karshen cin zalin da jami’an ‘yan sanda ke yi wa al’umma da ke gudana a jihar da ma wasu sassan Najeriya.

Talla

Jim kadan bayan fara wannan zanga zangar da ke daf da shiga mako na biyu ne dai wasu da ake kyautata zaton bata gari ne suka saje da masu zanga zangar, suka kuma fake da ita suna cin zarafin al’umma, ta wurin yi musu kwace da sace sace da kai hari kan jami’an yan sanda da kuma ofisoshin su.

A makon farko na wannan zanga zangar, sai da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi tattaki har wajen taron matasan da ke nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira cin zarafin alu’mma da jami’an SARS ke yi, ya ba su baki, ya kuma yi alkawarin mika korafe korafensu ga shugaban kasar.

Gwamna Sanwo-Olu ya cika wannan alkawari, inda a ranar ya nufi Abuja, fadar gwamnatin kasar, ya kuma mika bukatun masu zanga zanga hannu da hannu ga shugaba Muhammadu Buhari, yayin da kuma ya ziyarci Sufeto Janar na yan sandan kasar Muhammadu Adamu.

Rahotanni daga sassan birnin Lagos na nuna al’amura na dada tabarbarewa ganin yadda bata garin ke kaiwa jama’a hari suna kwace kayayyakin su, suna fasa musu motoci wani lokaci har da jikkata jama’a.

Ko a jiya litinin “yan Sandan basu tsira ba, inda aka kaiwa jami’an su hari aka kuma kwace musu kayan aiki a unguwar makoko dake Yaba.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da mana da kona ofisoshin ‘yan Sanda a wasu unguwannin dake birnin Lagos.

Sai dai wadannan masu zanga zanga sun ci gaba da gangamin nasu ba kakkautawa, lamarin da ya sa yanzu ta rikide zuwa tarzoma a wasu sassa na jihar Legas din.

A jiya Litinin, sai da wasu da ake zargi masu zanga zangar ne suka lalata tare da kona ofishin ‘yan sanda a yankin Yaba, baya ga lalata shaguna, suna awon gaba da dukiyar masu shi da sunan kwasar ganima.

A yau Talata, lamarin ya rincabe, inda dimbim matasa suka datse hanyoyi suna kona tayoyi a yankin Lagos Island, a dalilin haka ya zame wa ma’aikata, da ma wadanda suka fito sana’o’i dole su koma gidajensu.

Duk a Talatar nan, wasu gungun matasa da suka fito da sunan zanga zangar EndSARS, sun banka wa ofisoshin ‘yan sanda biyu wuta a unguwannin Orile da Amakoko.

Wasu sun samu munanan raunuka a cikin wannan tarzoma, zalika, akwai rahotannin da ke tabbatar da cewa mutum daya ya mutu unguwar Orile.

A halin yanzu ba a iya ketarawa zuwa tsibirin Legas saboda datse hanyoyi da masu zanga zangar suka yi.

Gabanin soma aiki da dokar hana fita a jihar Legas zuwa karfe 4 na yammacin Talata, jama’a da kansu sun takaita zirga zirgarsu saboda fargabar abin da ka iya aukuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.