Gurbacewar muhalli ta hallaka jarirai kusan 500 cikin shekara 1 - Bincike

Jarirai sabbin haihuwa
Jarirai sabbin haihuwa JUNI KRISWANTO / AFP

Wani binciken masana daga kasashen duniya ya bayyana cewar gurbacewar muhalli yayi sanadiyar mutuwar jarirai kusan 500,000 a shekarar da ta gabata, kuma akasarin su sun fito ne daga India da kasashen dake kudu da Sahara na Afirka.

Talla

Rahotan binciken yace kusan kashi biyu bisa uku na mutuwa ne sakamakon shakar iska mai guba dake fitowa daga man girki, inda a kasar India kawai aka samu mutuwar jarirai 116,000 dake watan farko bayan haihuwar su, sai kuma Afirka da aka samu jarirai 236,000.

Wannan bincike da Cibiyar Kula da lafiyar Amurka tare da Cibiyar Binciken Lafiya da Nazarin Cututtuka suka gudanar yace wadannan jarirai na mutuwa ne sakamakon shakar hayakin dake musu illa a cikin gidajen su.

Dan Greenbaum, shugaban Cibiyar Bincike ta HEI yace lafiyar jariri na da matukar tasiri ga makomar al’umma kuma wannan bincike ya dada fito da hadarin da jarirai ke fuskanta a wadannan yankuna guda biyu na Kudancin Asia da Yankin Afirka dake Kudu da Sahara.

Rahotan yace a fadin duniya baki daya, gurbacewar muhalli yayi sanadiyar kasha mutane miliyan 6 da dubu 700 a shekarar 2019, abinda ya nuna cewar itace hanya ta 4 da tafi hallaka jama’a a duniya bayan hawan jini da taba sigari da kuma cututtukan dake da nasaba da abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.