Afrika

An fitar da karin sakamakon zaben Guinea

Shugaban kasar Guinea Alpha Conde wanda ke kan hanyar lashe zaben kasar
Shugaban kasar Guinea Alpha Conde wanda ke kan hanyar lashe zaben kasar AFP

Hukumar zaben Guinea ta sanar da karin sakamakon zaben shugabancin kasar na wasu daga cikin manyan yankuna ko mazabunta, wadanda suka nuna shugaba mai ci Alpha Conde ne ke kan gaba, wajen lashe kuri’un da aka kada.Sanarwar na zuwa ne yayin da aka shafe kwanaki ‘yan adawa na tarzoma a sassan kasar dangane da zaben.

Talla

Sakamakon zaben da ya gudana na manyan yankuna 16 daga cikin jumillar 38 na kasar ta Guinea, shugaban hukumar zabe Kabinet Cisse ya bayyana, wanda kuma a fiye da rabin yankunan shugaba mai ci Alpha Conde ke kan gaba.

Zalika kafin sakamakon na baya bayan nan, kididdigar hukumar zaben ta nuna cewar shugaban Conden ne ya lashe mafi rinjayen kuri’un da aka kada a baki dayan manyan mazabun Conakry, babban birnin kasar ta Guniea.

Sai dai tun a ranar Litinin jagoran ‘yan adawa Cellou Dalein Diallo ya yi ikirarin lashe zaben shugabancin kasar, bisa dogara da sakamakon da wakilansa suka tattara daga rumfunan zabe.

Kawo yanzu dai rayukan mutane 9 ciki har da dan sanda 1 suka salwanta a fadan da ya barke tsakanin jami’an tsaro da ‘yan adawa, da ke yin Allah-wadai da aniyar shugaba Conde ta neman tazarcen wa’adi na 3, da suka ce hakan ya sabawa kundin tsarin mulki.

Wakilan kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS dake sa ido a zaben na Guinea sun bayyana gamsuwa da yadda ya gudana, duk da cewa bangaren ‘yan adawa sun dage kan zarginsu na cewar lallai an tafka magudi a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI