An gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Sudan
Mutum daya ya mutu a zanga zangar da aka gudanar a Sudan tare da gangami domin nuna bacin rai a game da tsadar rayuwa duk da tarin sojoji da ‘yan Sanda da aka girke domin ganin taron bai samu karsashi ba.
Wallafawa ranar:
Akalla masu zanga zanga 14 sun samu rauni, da dama suka samu matsalar numfashi sakamakon amfani da karfi fiye da kima da ‘yan sanda suka yi ta wajen jefa musu hayaki mai sa hawaye a babban birnin kasar Khartoum, a cewar jami’an kiwon lafiya
Masu rajin kare hakkokin jama’a suna kuma bukatar ganin an hukunta wadanda suka aikata laifin kisa lokacin juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin shugaba Omar Hassan Al Bashir.
‘Yan sand sun yi amfani da harsashen kwarai tare da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga zangar daga titunan da suka mamaye, inda a nan ne ma wani matashi mai shekaru 20 ya rasa ransa, biyo bayan samunsa da harsashi ya yi.
Kungiyar kwararrun ma’aaikata ta Sudan ce ta shirya wannn gangami, ita ce ma ta shirya zanga zangar da ta yi sanadin kifewar gwamnatin shugaba Omar al-Bashir a watan Afrilun shekarar da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu