Najeriya

Masu tarzoma sun kai hari tashar yan Sanda a Igando

Masu tarzoma a birnin Lagos yau sun kai hari tashar Yan Sandan dake Igando inda suka kwashi makamai, yayin da suka yi kokarin fasa gidan yarin Ikoyi kafin jami’an tsaro su tarwatsa su.

Wasu daga cikin masu tarzoma a Lagos
Wasu daga cikin masu tarzoma a Lagos AP/Sunday Alamba
Talla

Rahotanni daga tashar yan Sandan dake Igando sun ce masu zanga zangar sun raunata Baturen Yan Sandan tashar, CSP Taiwo Kasumu lokacin da yake jagorancin jami’an sa kusan 200 domin kare ofishin, yayin da suma suka raunata wasu daga cikin su.

Daga bisani masu zanga zangar sun fi karfin jami’an Yan Sandan, wadanda suka kutsa kai suka kwashe bindigogi da motoci guda 2 da wasu kayan aiki kafin bata garin su cinnawa ofishin wuta, yayin da su kuma matasan suka kwashi wasu.

A unguwar Ikoyi anyi arangama tsakanin jami’an tsaron soji da Yan Sanda wadanda suka hana wasu matasa dauke da makamai kokarin kutsa kai wajen fasa gidan yarin dake unguwar.

Jami’an tsaron sun yi nasarar dakile harin da kuma tarwatsa maharan kamar yadda kakakin rundunar Yan Sandan jihar Muyiwa Adejobi ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI