Najeriya

Mun saurari korafe-korafenku- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci matasan dake zanga zanga da su kaurace wa tituna domin tattaunawa da gwamnati da zummar shawo kan matsalolin da suka addabe su.

Talla

A jawabin da ya yi wa al’ummar kasar karo na farko tun bayan barkewar zanga- zangar adawa da cin zarafin da 'yan Sanda ke yi, shugaban ya ce sun ji korafe korafen da matasan ke yi, kuma suna daukar matakan gyara saboda haka su kaucewa daukar matakan da zasu yiwa tsaron kasa barazana.

Shugaban wanda ya bayyana damuwa kan irin tarzomar da ta biyo bayan zanga- zangar yace gwamnatin sa ta gabatar da shirye shirye da dama domin inganta rayuwar matasa.

Buhari ya ce yayin da gwamnati ta gamsu da ‘yancin mutane na gudanar da zanga- zanga, dokar kasa ta kuma bukaci mutunta ‘yanci sauran jama’a da su gudanar da harkokin su bisa doka.

Shugaban ya ce gwamnatin sa ta amince da bukatun matasan guda 5 da kuma soke rundunar SARS a karkashin shirin yin garambawul ga aikin ‘yan sanda amma sai wasu suka ki fahimtar matsayin gwamnati wajen kaddamar da hare - hare kan gidajen yari da dukiyoyin gwamnati da kai hari gidan Babban Basaraken Lagos mai son zaman lafiya da kuma tashar jiragen saman kasa.

Buhari ya ce ya kadu sosai da rasa rayukan da aka samu, kuma babu dalilin danganta wadannan abubuwa da bukatun masu zanga - zangar da kuma yada labaran karya cewar gwamnati ba ta damu da halin da jama’a suke ciki ba.

Shugaban ya ce gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen biyan bukatun al’ummar kasar duk da matsalolin da take fuskanta na rashin kudi sakamakon annobar korona da kuma kokarin su na fitar da mutane miliyan 100 daga cikin talauci nan da shekaru 10.

Buhari ya ce zasu ci gaba da tabbatar da hadin kan kasa da bunkasa shugabanci na gari da harkokin dimokiradiya wajen tattaunawa da kuma tabbatar da ‘yancin kowanne dan kasa, yayin da ya jaddada hakkin gwamnati na kare lafiya da dukiyoyin jama’a.

Shugaba Buhari ya kuma bukaci makotan Najeriya da kasashen duniya da suka bayyana matsayin su kan halin da ake ciki a kasar da su dinga bincike domin sanin gaskiyar abinda ke faruwa kafin rugawa su yanke hukunci akai cikin gaggawa.

Daga karshe shugaban ya bukaci masu zanga zanga da su rungumi shirye shiryen da wannan gwamnati ta dauka na inganta rayuwar su da kuma kaucewa barin bata gari na amfani da su wajen haifar da rudani da zummar rusa dimokoiradiyar kasa.

Shugaban yace yin haka zai yi tsaron kasa illa kuma babu dalilin da zasu amince da haka, yayin da ya bukaci matasan da su cigaba da tattaunawa da gwamnati domin samo maslaha a daidai lokacin da ya bukaci jami’an tsaro da su kare lafiyar jama’a da kuma dukiyoyin su.

Buhari ya kuma godewa Gwamnoni da shugabanni addini da sarakuna da kuma mutanen da suka yi ta kiran samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, yayin da ya sha alwashin mutunta ‘yancin kowanne dan kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.