Najeriya

Najeriya:'Yan bindiga sun halaka mutane 22 a Zamfara

'Yan bindiga sun dade suna cin karensu ba babbaka a wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya.
'Yan bindiga sun dade suna cin karensu ba babbaka a wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya. Daily Trsut

Wasu yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a kauyen Tungar kwana na karamar hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara tare da kashe akalla mutane 22 lokaci guda.Faruk Mohammad Yabo ya jiyo mana mutanen kauyen na cewar wannan harin shine karo na uku da ake kai masu duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar ke cewa tana yi da yan bindigar.