Trump ya katse hira da talabijin saboda tambayoyi masu zafi
Wallafawa ranar:
Shugaban Amurka Donald Trump ya haure takalman sa ya fice daga wajen hira da talabijin din CBS saboda abinda ya kira nuna son kai wajen tambayoyin da masu hira da shi suka jefa masa.
Shugaban ya sanar da kafar twitter cewar a shirye yake ya gabatar da hirar da ya nada kafin kafar talabijin ta gabatar da na ta domin nuna yadda yar Jaridar Leslie Stahl ta dinga nuna masa san kai da kiyaya da kuma rashin kunya.
Hotan bidiyon da aka sanya a shafin Facebook na shugaban sabanin yarjejeniyar da fadar White House ta shiga da CBS ya nuna yadda abin ya faru daga farko har karshe.
Faifan ya nuna Stahl bata daga muryar ta ba ko kuma katse shugaban, sai dai kalubalantar wasu daga cikin amsoshin da ya gabatar musamman yadda ya tinkari anobar korona da yadda magoya bayan sa ke musgunawa abokan hamayar sa da wasu batutuwa masu muhimmanci.
Shugaba Trump yayi zargin cewar tashar CBS da wasu kafofin yada labarai basa yiwa abokin adawar sa tambayoyi masu karfi lokacin hira da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu