Rikicin - Libiya

An kulla yarjejeniyar tsagaita wuta na dindindin a Libiya

Bangarorin dake hammaya da juna a Kasar libya sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta na dindindin
Bangarorin dake hammaya da juna a Kasar libya sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta na dindindin Violaine Martin / UNITED NATIONS / AFP

Bangarorin dake hammaya da juna a Kasar libya sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta na dindindin bayan shafe tsawon kwanaki biyar suna gudanar da tattaunawar sulhu a ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake birnin Geneva.

Talla

Stephanie Williams, manzo ta musamman ce na Majalisar dinkin duniya zuwa ga libya dake yankin arewacin Afrika, ta ce yau babbar rana ce ga alummar Kasar da aka shafe tsawon shekaru ana gwabza yaki tsakanin bangarorin gwamnatin da dakarun dake marawa Khalifa Haftar baya.

Stephanie ta ce da misalin karfe 11:15 na safiyar yau a shelkwatar Majalisar dinkin duniya dake Geneva, bangarorin dake hammaya da juna suka kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a fadin kasar na dindindin, wadda ba tare da bata lokaci ba zai soma aiki.

Kana tace bangarorin sun amince daukacin dakarun Kasar da 'ya'yan kungiyoyi masu rike da makamai su koma sansanoninsu, bayaga haka sun Kuma dibawa baki mayaka tsawon watanni 3 su fice daga illahirin yankunan Kasar da suka mamaye.

An dai shafe kusan shekaru 10 ana gwabza yaki a Libya tun bayan kifar da gwamnati tare da kashe shugaban Kasar a waccan lokaci moammer Khadhafi, abinda ya sa kungiyoyin mayaka suka mamaye kasar.

Saidai a watan agustan da ya gabata ne bangarorin biyu dake rikici da juna suka sanar da Shirin tsagaita wuta wadda a yau aka kawo karshen shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.