Najeriya

Shugaba Buhari na ganawa da tsoffin Shugabanin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo da Abdusalami Abubakar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo da Abdusalami Abubakar Femi Adesina/Facebook

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan da ya yi jawabi ga yan kasar ,ya gayyaci tsofin shugabanin kasar a fadar sa dake Abuja don duba hanyoyin kawo karshen zanga-zangar da wasu yankunan kasar suka fada.

Talla

A jawabi da ya gabatarwa yan Najeriya ,Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bukaci jama'a da su kai zuciya nesa,gwamnati na iya kokarin ta don shawo kan matsalolin da jama'a ke fuskanta  a cewar sa,yayinda tsohon Shugaban Najeriya Abdusalami Abubakar ya bayyana damuwa kan tarzomar da ta biyo bayan zanga zangar matasa inda ya bukaci kai zuciya nesa.

Jama'a sun nuna matukar kaduwa a wasu yankuna ,musaman irin su Lagas inda a yanzu jami'an tsaro ke ci gaba da suturi a wasu unguwani domin sake dawo da zaman lahiya.

Yayin ganawa da manema labarai, tsohon shugaban Najeriya Abdusalami Abubakar ya kuma bayyana damuwa kan yadda ake yada labaran karya ta hanyar yanar gizo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.