Amurka-Sudan

Sudan zata kulla huldar diflomasiya da Israila - Trump

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, da shugaban rikon kwaryar Sudan Abdel Fattah al-Burhan.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, da shugaban rikon kwaryar Sudan Abdel Fattah al-Burhan. Sudanese Cabinet via AP, File

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar kasar Sudan ta amince ta kulla huldar diflomasiya da Israila, yayin da yace nan gaba kadan wasu Karin kasashen larabawa guda 5 za suyi haka.

Talla

Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana kulla huldar tsakanin Sudan da Israila ne a daidai lokacin da yake shirin cire sunan kasar cikin jerin kasashe masu goyan bayan ayyukan ta’addanci a duniya, abinda Sudan ke bukata ruwa a jallo.

Jami’an fadar shugaban Amurka sun raka Yan Jaridu zuwa ofishin shugaba Trump lokacin da yake Magana ta waya da shugabannin Sudan da kuma Firaministan Israila Benjamin Netanyahu aka sa musu su saurara, kamar yadda wani jami’in fadar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Netanyahu ya shaidawa Trump cewar suna dada fadada shirin zaman lafiyar su cikin gaggawa tare da jagorancin sa, yayin da shugaba Trump yace akwai wasu Karin kasashe da zasu taho nan gaba kadan.

Sanarwar da fadar shugaba Trump ta gabatar bayan taron ya bayyana wannan mataki a matsayin gagarumar cigaba, yayin da Firaministan Sudan Abdullah Hamdok ya godewa Trump dangane da yunkurin cire kasar daga cikin masu taimakawa ayyukan ta’addanci ba tare da cewa komai dangane da dangantaka da Israila ba.

Daga cikin kasashen da Trump ke cewa yana fatar zasu kulla hulda da Israilar harda Saudi Arabia amma shugabannin ta sun ki cewa komai dangane da lamarin, yayin da gwamnatin kasar a baya tace lokaci bai yi ba tukuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI