Afrika

Alpha Conde ya lashe zaben kasar Guinea Conakry

Shugaban kasar Guinea Alpha Conde a birnin Conakry
Shugaban kasar Guinea Alpha Conde a birnin Conakry AFP

Hukumar zabe a kasar Guinea ta bayyana shugaba Alpha Conde a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da akayi a makon jiya, inda ya samu sama da kashi 59 na kuri’un da aka kada, yayin da abokin karawar sa Cellou Dalein Diallo ya samu sama da kashi 33 da rabi.

Talla

Shugaban hukumar Kabinet Cisse ya gabatar da sakamakon wanda zai baiwa shugaba Conde damar yin wa’adi na 3 duk da korafe korafen da wasu al’ummar kasar ke yi.

Sakamakon zaben na zuwa ne bayan tashe tashen hankulan da aka samu wadanda suka yi sanadiyar hallaka akalla mutane 10 a cikin mako guda.

Yanzu hankali ya koma wajen kotun fasalta kundin tsarin mulki wadda ake saran ta amince da sakamakon kafin a rantsar da shugaba Conde.

Shugaban Yan adawa Cellou Diallo ya sha alwashin kalubalantar sakamakon zaben a kotu saboda abinda ya kira tafka magudi.

Kafin dai bada sakamakon, Diallo ya bayyana cewar shi ya samu nasara kafin Hukumar zabe ta fito fili tayi watsi da ikrarin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.