Afrika

An fara gudanar da zaben ‘yan majalisu a Masar

Shugaban Masar Abdel Fattah Al-Sissi da wasu yan siyasa
Shugaban Masar Abdel Fattah Al-Sissi da wasu yan siyasa Présidence égyptienne / AFP

Yau ake gudanar da zaben ‘Yan Majalisu a kasar Masar wanda ake bayyana shakku ko Jam’iyyar shugaba Abdel Fattah al Sisi na iya samun rinjaye da take bukata.

Talla

Tuni aka bude tashoshin zabe inda ake saran mutane akalla miliyan 63 su kada kuri’a wajen zaben ‘Yan Majalisu 568, yayin da shugaba al Sisi zai nada sauran 26 da zasu cike gibin kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Zaben zai gudana ne kashi biyu, yayin da za’a gudanar da shi a Yankuna 14 yau da gobe, sai kuma Yankuna 13 cikin su harda Birnin Alkahira a ranakun 7 da 8 ga watan gobe.

Majalisar dake barin gado da aka zaba a shekarar 2015 tana kunshe ne da tarin magoya bayan shugaba al Sisi, yayin da ‘yan adawa ba su wuce 25 zuwa 30 ba.

‘yan takara sama da 4,000 ke fafatawa a wannan zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI