Guinea

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci tattaunawa a tsakanin 'yan siyasar Guinea

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Lisi Niesner

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci Yan siyasar Guinea da su hau teburin tattaunawa domin kawo karshen rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 10.

Talla

Sanarwar da Guterres ya bayar ta ce a shirye Majalisar take ta jagoranci tattaunawa tsakanin bangarorin dake rikicin domin tabbatar da zaman lafiya cikin gaggawa.

Guterres ya bukaci shugaba Alpha Conde da ya lashe zaben shugaban kasa da shugaban 'yan adawa Cellou Dalein Diallo da su janyo hankalin magoya bayan su domin kauce wa tashin hankali a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.