Najeriya

Mutane 69 aka kashe a tarzomar Najeriya - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Nigeria/presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar mutane 69 suka mutu sakamakon tarzomar da aka samu lokacin zanga zangar adawa da cin zarafin yan Sanda, yayin da 37 suka samu raunuka, kuma adadin ya hada da fararen hula da jami’an yan Sanda da kuma soji.

Talla

Buhari ya bayyana haka ne lokacin taron da ya gudanar da taron tsoffin shugabannin kasar da kuma hafsoshin tsaro domin shaida musu halin da ake ciki da kuma irin matakan da gwamnati ke dauka.

Shugaban kasar yace daga cikin mutane 69 da aka tabbatar da mutuwar su, 51 fararen hula ne, yayin da kuma aka samu jami’an Yan Sanda 11 da sojoji guda 7.

Buhari ya shaidawa tsoffin shugabannin irin matakan da gwamnatin sa ta dauka na amincewa da bukatun masu zanga zangar da aiwatar da sauye sauye a bangaren aikin yan Sanda wanda ya kai ga rusa rundunar SARS da suke adawa da shi, amma sai wasu suka karbe ragamar zanga zangar inda suka fara tarzoma da kai hari kan jami’an tsaro da fararen hula da kuma dukiyar jama’a, inda aka dinga cinnawa gine gine wuta da sace dukiyar jama’a.

Rahotanni sun ce tarzomar ta bazu zuwa Jihohi da dama inda aka dinga kai hare hare musamman kan baki da sace dukiyar jama’a, abinda ya sa gwamnatocin jihohi da dama suka kafa dokar hana fita ta sa’oi 24.

A jawabin da ya yiwa al’ummar jihar sa yammacin jiya, Gwamnan Rivers Nyesom Wike ya jaddada matsayin sa na haramcin kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra da kuma sanya tukuici kan kamo daya daga cikin shugabannin ta da ake zargi da haifar da tashin hankali da hare hare a jihar.

Yanzu haka hukumar kare hakkin Bil Adama ta kasa ta kaddamar da bincike kan lamarin, inda ta bukaci jama’a su gabatar da korafe korafen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.