Wasanni

Na gode Brazil - Pele

Pelé,Sarkin kwallon kafa na Duniya
Pelé,Sarkin kwallon kafa na Duniya REUTERS/Christian Hartmann/File Photo

Tsohon tauraron kwalon kafar duniya Edson Arantes do Nascimento da aka fi sani da Pele ya bayyana godiyar sa da yadda mutanen Brazil da kasashen duniya suka dinga aike masa da sakon fatan alheri lokacin da cika shekaru 80 a duniya jiya juma’a.

Talla

Pele ya bayyanawa al’ummar kasar cewar yana cikin halin lafiya duk da jinyar da yayi a kwanakin baya, yayin da yace ba zai iya buga kwallo ba a sakon da ya aike ta faifan bidiyo.

Tsohon tauraron ‘dan wasan duniyan da ya lashe kofin duniya sau 3 a shekarar 1958 da 1962 da 1970 ya zabi gudanar da bikin cika shekaru 80 a asirce da iyalan sa kamar yadda ya saba yi kowacce shekara, amma kuma mutane sun shirya bukukuwa da dama a Brazil domin girmama gwarzon na su da suka hada da nuna kayan tarihi a Sao Paulo inda ya fara wasan kwallon sa a shekarar 1955 lokacin yana da shekaru 15.

Pele ya kuma rera wata waka da wasu fitattun mawakin Mexico Rodrigo da Gabriela a matsayin kyauta ga masu kaunar sa da kuma shi kan sa, yayin da ya aike da sako ta Instagram inda yake godewa Brazil da mutanen Brazil.

Tsohon tauraron Yan wasan yace kullum yana cikin farin cikin sanya rigar kwallon Brazil, kuma ya godewa masu goyan bayan sa, yayin da ya sanya hotan sa lokacin da yake murnar jefa daya daga cikin kwallaye 1,281 da ya zirara a raga.

Ganin irin rawar da ya taka wajen daga darajar kwallo da kuma nasarorin da ya samu ya sa FIFA ta nada a matsayin ‘dan wasan da yafi kowa fice a karni na 20 a shekara ta 2000 tare da Diego Maradona na Brazil, lokacin da ya cika shekaru 60 da haihuwa a duniya.

An dai haifi Pele ne ranar 23 ga watan Oktobar shekarar 1940 a birnin Tres Coracoes dake kudu maso gabashin Brazil, kuma yanzu haka halin lafiyar sa na cigaba da tabarbarewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI