Najeriya

Firsinoni sama da 2.000 suka tsere a Najeriya

Wasu daga cikin firsinoni dake tsare a gidan yari
Wasu daga cikin firsinoni dake tsare a gidan yari EL SALVADOR'S PRESIDENCY PRESS OFFICE / AFP

Tarzomar da ta barke a Najeriya sakamakon zanga zangar adawa da cin zarafin Yan Sanda ta sanya firsinoni sama da 2,000 tserewa daga gidajen yarin da ake tsare da su a sassan kasar.

Talla

Rahotanni sun ce firsinonin wadanda wasu daga cikin su masu aikata manyan laifuffuka ne sun tsere ne daga gidajen yarin Benin dake Jihar Edo da Akure dake Jihar Ondo, kuma yawan su ya kai 2,051, yayin da jami’an tsaro suka yi nasara dakile kokarin fasa gidan yarin Ikoyi dake Lagos domin sakin wasu firsinonin.

Masu sa ido kan harkokin tsaro a Najeriya sun bayyana matukar damuwa kan tserewar wadannan firsinoni wadanda suka zama hadari ga jama’a.

Rahotanni daga sassan Najeriya na nuna cewar tarzomar na cigaba da daukar sabon salo inda ake fasa dakunan aje abinci na gwamnati da na jama’a ana dibar ganima.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.