'Yan aware - Kamaru

MDD da AU sun yi Allah wadai da kisan dalibai a Kamaru

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Afirka sun yi Allah wadai da yadda wasu Yan bindiga suka bude wuta kan daliban makaranta a Kumba dake kasar Kamaru, inda suka kashe dalibai guda 8.

Yankin Bafang dake yammacin kasar daf da yankin yan aware
Yankin Bafang dake yammacin kasar daf da yankin yan aware Radio Site Dar
Talla

Kungiyar agaji ta OCHA tace an kai harin ne a makarantar da ake kira Mother Francisca inda yan bindigar suka yi amfani da bindigogi da adduna wajen hallaka yaran.

Wannan kazamin hari na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke cigaba da fuskantar rikicin Yan aware dake kai haree hare lokaci zuwa lokaci.

Wata majiya tace adadin maharan ya kai 9, yayin da yanzu haka wasu yara 12 ke kwance a asibiti sakamakon raunukan da suka samu.

Malachie Manaouda, ministan lafiyan Kamaru yayi Allah wadai da harin na Kumba wanda ya bayyana shi a matsayin abin tada hankali.

Shugaban kungiyar kasashen Afirka Moussa Faki Mahamat yace babu kalaman da zasu bayyana irin alhinin sa dangane da kazamin harin da aka kaiwa yara kanana dake neman ilimi.

Rikicin yan aware a Kamaru yayi sanadiyar hallaka mutane sama da 3,000, yayin da sama da 700,000 suka tsere daga gidajen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI