Najeriya

Mutane 11 sun mutu a tirmitsitsin kwashe abinci

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Najeriya
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Najeriya UnEarthical/via REUTERS

Akalla mutane 11 aka tabbatar da mutuwar su a sassan Najeriya sakamakon tirmitsitsin kwasar abincin da aka jibge a dakuna aje kayayayki na gwamnati a Jihohin Edo da Taraba da kuma Anambra, abinda ya sa gwamnatocin wasu jihohi kafa dokar hana fita na sa’oi 24.

Talla

Matasa masu ji da karfi da suka kunshi maza da mata sun kwashe karshen mako suna fasa wuraren ajiyar abincin gwamnati da aka sanya tallafin taimakawa jama’a saboda annobar korona suna kwashewa zuwa gidajen su.

Rahotanni sun ce bayan Lagos da Osun da aka fara samun matsalar, an kuma samu a Jihohin Edo da Anambra da Kaduna da Plateau da Cross Rivers da kuma Ekiti.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya tace mutane 5 sun mutu a Jihar Taraba lokacin da suke kokawar kwashe wasu jakankunan kudi guda 2 dake dauke da tarin kudade a dakin aje abinci, abinda ya sa gwamnati ta kafa dokar hana fita na sa’oi 24.

Ita ma gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa irin wannan doka a fadin Jihar sakamakon matsalar da aka samu a Barnawa lokacin da matasa suka fasa shagunan aje kayan abinci da unguwar Talabishan.

A jihar Plateau, matasan sun fasa inda aka aje kayan abincin da gwamnatin tarayya ta kai makon jiya domin rabawa mata inda suka kwashe, abinda ya sa gwamnatin ta kafa dokar hana fita ta sa’oi 24 da kuma bayanin cewar kayan wanda ministan jinkai Sadiya Umar ta kai jihar ne makon jiya amma zanga zanga ta hana raba su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.