Cote d'Ivoire

Rikicin siyasa ya haddasa mutuwar mutane a Cote D'Ivoire

Yan Sanda na tarwatsa masu zanga-zanga  a Abidjann
Yan Sanda na tarwatsa masu zanga-zanga a Abidjann Issouf SANOGO / AFP

Rahotanni daga garin Dabou na kasar Cote D’Ivoire dake da nisan kilometa 50 yammacin birnin Abidjan na nuni cewa fadan kabilanci da ya auku a farkon makon nan mai karewa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 16 inda wasu 67 suka samu rauni.

Talla

Hukumomin sun bayanna kama kusan mutane 52 da tarin makamai da suka hada da bindigogi da aduna.

Domin dawo da zaman lafiya a yankin, gwamnatin ta kafa dokar ta baci zuwa yau lahadi. A daya Geffen Shugaban kasar Alassane Ouattara ya ce zai bari tsohon shugban kasar Laurent Gbagbo wanda yanzu haka yake fuskantar tuhumar laifukan yaki a kotun hukunta manyan laifuka a birnin Hague ya dawo gida bayan kammala zaben shugaban kasa na mako mai kamawa.

Sai dai Shugaba Ouattara yace babu abinda ya dace ga tsohon Shugaban majalisa kuma tsohon Firaminista Guillaume Soro banda zama kurkuku iya rayuwar sa .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.