Isra'ila zata tallafawa Sudan da abincin da ya kai dala miliyan 5

Franministan Isra'aila Benjamin Netanyahu
Franministan Isra'aila Benjamin Netanyahu Sebastian Scheiner/Pool via REUTERS

Kasar Israila tace zata aikawa Sudan da alkamar da ta kai ta Dala miliyan 5 kwanaki bayan kulla yarjejeniyar huldar dangantaka a tsakanin su kamar yadda shugaba Donald Trump ya sanar.

Talla

Ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewar bukatar su itace samun dangantaka mai karfi tsakanin kasashen biyu, abinda ya sa zasu aike da alkamar kenan.

Netanyahu ya kuma ce Israila zata hada kai da Amurka wajen inganta dimokiradiya a Sudan.

A makon da ya gabata shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar kasar Sudan ta amince ta kulla huldar diflomasiya da Israila, yayin da yace nan gaba kadan wasu karin kasashen larabawa guda 5 za suyi haka.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana kulla huldar tsakanin Sudan da Israila ne a daidai lokacin da yake shirin cire sunan kasar cikin jerin kasashe masu goyan bayan ayyukan ta’addanci a duniya, abinda Sudan ke bukata ruwa a jallo.

A halin da ake ciki, yunkurin gwamnatin Sudan na kulla yarjejeniyar huldar diflomasiya da Israila ya raba kan mutanen kasar, abinda ya sa wa suke zargin shugabannin da cin amanar kasa, yayin da wasu kuma ke kallon matakin a matsayin wanda zai taimaka wajen ceto kasar daga matsalar tattalin arziki.

Wani masanin kasar Othman Mirghani yace abinda gwamnatin kasar ta mayar da hankali akai shine bunkasa tattalin arzikin kasa wanda ake saran samu bayan cire sunan kasar daga masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci, amma sai Amurka ta tilastawa Sudan kulla hulda da Israila kafin cire sunan ta, duk da biyan diyyar sama da Dala miliyan 300 ga Amurkawa.

Wasu kuma Yan kasar na kallon matakin a matsayin cin amanar Falasdinawa wadanda Israila ke cigaba da mamaye filayen su.

 

 

 

 

J

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.