FARANSA - MALI

Le Drian na ziyarar aiki a Mali

Dakarun Faransa na Barkhan a Mali
Dakarun Faransa na Barkhan a Mali Alain JOCARD / AFP

Ministan Harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya fara ziyarar aiki a Mali domin bunkasa dangantaka da gwamnatin rikon kwaryar kasar domin ganin ta aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a kasar Algeria.

Talla

Le Drian ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, muhimmancin ziyarar itace tabbatar da yarda a tsakanin bangarorin biyu da zummar ganin sun yi aiki tare.

Ministan ya kuma ce zasu tattauna kan yaki da cin hanci da rashawa da yaki da yan ta’adda a karkashin rundunar G5 Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.