Najeriya

Buhari keda hurumin hukunta sojoji-Sanwo Olu

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu
Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu LASG

Gwamnan jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya, Babajide Sanwo-Olu ya ce gwamnati na yin dukkan mai yiwuwa wajen binciken sojojin da suka aikata kisan kiyashi a Lekki yayin zanga-zangar bukatar rusa rundunar SARS da ta juye zuwa rikici a sassan kasar.

Talla

Gwamnan Lagas Sanwo-Olu a zantawarsa da manema labarai a yankin,ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ne kadai ke da cikakken zarafin tabbatar da ganin an hukunta masu hannu a kisan.

A cewar Gwamnan na Lagos, za su bibiyi hotunan da na’urori suka nada don gano Sojin da suka yi aika-aikar.

Kusan mako daya da tarzomar yayin ganawa da manyan hafsoshin sa da suka hada da kwamandodin dake kula da rundinoni daban daban, Janar Buratai yace ba zasu lamincewa rashin biyayay daga kowanne jami’in sojin ba, inda ya bukace su da su shaidawa rundunonin su muhimmancin kare demokiradiya da kuma cigaban kasa.

Sanarwar da rundunar sojin ta gabatar mai dauke da sanya hannun Daraktan yada labarai Kanar Sagir Musa tace sojojin na kan bakar su cewar mulkin dimokiradiya shine mafi inganci saboda haka ya zama wajibi su kare shi.

Sanarwar ta ruwaito Janar Buratai na cewar irin abubuwan da suka faru a cikin ‘yan kwanakin nan sun tabbatar da cewar wasu bata gari na neman wargaza Najeriya ta kowanne hali.

Shugaban rundunar sojin yace tun farko sun fahimci cewar zanga zangar yaki da cin zarafin Yan sanda wani yunkuri na shafawa sojin kashin kaji da kuma bata sunan su da na gwamnati, domin tinzira jama’a su musu bore.

Janar Buratai yace wadannan bata garin tare da masu goyan bayan su a gida da waje sun kisa batawa sojin suna wajen kokarin sun a tabbatar da bin dokar hana fita da hukumomin Lagos suka saka da wasu jihohi, yanzu kuma sun koma suna zargin sojoji kan ayyukan da bata gari keyi duk da shaidun da suka bayyana karara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.