Najeriya

Buhari ya sake nada Farfesa Mahmood Yakubu a INEC

Yakubu Mahmood Shugaban hukumar zaben Najeriya
Yakubu Mahmood Shugaban hukumar zaben Najeriya News Express Nigeria

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake nada Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zaben kasar bayan kamala wa’adin sa na farko.

Talla

A wasikar da ya aikewa shugaban Majalisar Dattawa sanata Ahmed Lawal, Buhari yace nadin ya dace da Sashe na 154 sakin layi guda na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999.

Sanarwar da mai bashi shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya rabawa manema labarai tace shugaba Buhari ya fara nada Farfesa Mahmood ne a watan Nuwambar shekarar 2015 domin maye gurbin Farfesa Attahiru Jega.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.