Bakonmu a Yau

Burinmu shine kowane dan Africa ya mallaki mahallin kansa - Shelter Afrique

Wallafawa ranar:

Kamfanin Shelter Afrique, kamfani ne da aka kafa a nahiyar Afirka dake da rassa 44, wadda ke mayar da hankali wajen ganin al’ummar nahiyar sun mallaki muhalli na kan su.Cibiyar wannan kamfani na Nairobi dake kasar Kenya, kuma Dr Mohammed Gambo, dan Najeriya, na daya daga cikin manajojin kamfani dake kula da tsare tsare da bincike da kuma hadin kai.Shugaban Sashen Hausa Robert Minangoy ya tattauna da shi a Ofishin sashen Swahili dake Nairobi kan ayyukan da suke na taimakawa ‘yan Afirka wajen samun gidaje ko kuma inganta wadanda suke da shi, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.

Dr. Gambo, daya daga cikin manajojin kamfanin Shelter Afrique.
Dr. Gambo, daya daga cikin manajojin kamfanin Shelter Afrique. RFI Hausa\R. Minangoy
Sauran kashi-kashi