Wasanni

Josep Maria Bartomeu ya sauka daga mukamin sa

Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu.
Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu. REUTERS/Albert Gea

Shugaban Kungiyar kwallon kafar Barcelona Josep Maria Bartomeu ya sauka daga mukamin sa sakamakon matsin lamba daga ciki da wajen kungiyar dangane da takaddamar sa da Lionel Messi.

Talla

Bartomeu wanda ya hau kujerar a shekarar 2014 na fama da yunkurin tsige shi daga magoya bayan kungiyar tun bayan lokacin da Messi ya gabatar da takardar sa na neman barin kungiyar.

Murabus din Bartomeu na zuwa ne kwanaki 3 bayan Real Madrid ta lallasawa barcelona duka da ci 3-1 a Camp Nou a gasar La Liga.

Messi ya zargi tsohon shugaban da yaudarar sa lokacin da kungiyar ta hana shi barin kungiyar a karshen kakar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.