Afrika

An sace wani Ba'Amarike a Massalata dake Nijar

Wasu daga cikin masu garkuwa da jama'a
Wasu daga cikin masu garkuwa da jama'a The Nation

A Kasar Nijar ana samun rahotannin satan mutane ana garkuwa da su don neman kudaden fansa duk da matakan tsaro da hukumomin kasar ke dauka don hana irin wannan matsala.Koda a jiya Littini sai da aka sami wasu da suka sace wani Ba-Amarike a yankin Massalata dake jihar Tahoua, suka tafi dashi kuma har yanzu babu wanda ya san inda yake.Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Moussa Aksar dan jarida a kasar Niger mai sharhi dangane da harkokin tsaro ko yaya yake kallon wannan matsala a Niger.