Wasanni-Kwallon kafa-Covid 19

Shugaban Fifa ya kamu da Covid -19

Gianni Infantino ya kamu da kwayar cutar Covid-19 kamar dai yada wata sanarwa daga hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta fitar,da samun wannan labari Shugaban na Fifa ya killace kan sa kamar dai yada aka bukaci a yi. 

Gianni Infantino, Shugaban hukumar kwallon kafa ta Fifa
Gianni Infantino, Shugaban hukumar kwallon kafa ta Fifa Attila KISBENEDEK / AFP
Talla

Gianni Infantino mai shekaru 50 na daga cikin manyan jami'an hukumar kwallon kafar ta Duniya da aka sanar da sun kamu da wannan cuta,wanda yanzu haka likitoci suka bukaci duk wandada suka kusanci Infantino da a gudanar da gwaji a kan su.

Wannan cuta ta kawo cikas ga wasannin kwallon kafa a kasashen Duniya,kazzalika an gano wasu yan wasa da suka kamu da cutar.

A shekara ta 2016 ne ya lashe zaben shugabancin  Fifa, Infantino ya samu kuri’u 115 a zagaye na biyu na zaben wanda aka gudanar a birnin Zurich na kasar Switzerland  yayin da Salman ya samu kuri’u 88.

Infantino mai shekaru 50 ya yi alkawarin jagorantar hukumar da sabon salo bayan ta gamu da badakalar cin hanci da rashawa wadda ta zubar da kimarta a idan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI