Sudan

Cire tallafin mai ya haddasa ninkuwar farashin Fetur a Sudan

Wani gidan mai a birnin Khartoum na Sudan.
Wani gidan mai a birnin Khartoum na Sudan. ASHRAF SHAZLY / AFP

Gwamnatin Sudan ta sanar da cire tallafin man fetur wanda ya sanya ninkuwar farashin man a sassan kasar, batun da ake fargabar ya iya haddasa yamutsi.

Talla

Baya ga farashin man, nau’ikan sinadaran iskar gas da sauran man dizel da Sudan kan siyo daga ketare sun linka kudinsu yayinda wasu suka ribanya sau biyu.

Matakin dai a cewar gwamnatin kasar wani yunkuri ne na rage gibin kasafin kudin da aka samu, sai da alamu tuni batun ya fara harzuka al’umma.

Mukaddashin ministan makamashi na Sudan Khayry Abd-al-Rahman ya shaidawa taron manema labarai a Khartoum cewa farashin man da kasar ke sayowa daga ketare zai koma dala 2 da centi 1 kan duk lita guda yayinda man fetur da kasar ke tacewa za a rika sayar da shi kan dala 1 kowacce lita.

Sudan wadda ke fuskantar karancin man fetur, sabuwar gwamnatin kasar na kokarin daidaita al’amura da kuma farfado da tattalin arziki da ya fuskanci koma baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.