Guinea-EU

EU ta diga ayar tambaya kan sahihancin sakamakon zaben Guinea

Shugaban kasar Guinea Alpha Conde a birnin Conakry
Shugaban kasar Guinea Alpha Conde a birnin Conakry AFP

Kungiyar Tarayyar Turai ta diga ayar tambaya game da sahihancin sakamakon zaben Guinea da ya bayyana Alpha Conde a matsayin wanda ya yi nasara.

Talla

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta goyi bayan fafatukar da kungiyoyin Tarayyar Afrika ECOWAS da kuma Majalisar Dinkin Duniya ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Acewar EU duk da ya ke an gudanar da zaben na Guinea cikin lumana amma akwai shakku kan nasarar Alpha Conde da ke kokarin jan ragamar kasar zuwa zagaye na 3 bayan gyara a kundin tsarin mulki da ya bashi damar ci gaba da mulki.

EU ta bayyana cewa bayanan da ta ke samu daga mambobinta da suka sanya idanu a zaben kasar da mabanbantan ‘yan siyasar da aka zanta da su ciki har da jagoran adawar kasar Cellou Dalein Diallo da ke ci gaba da fuskantar daurin talala a cikin gidansa, ya nuna akwai lauje cikin nadi kan nasarar ta Alpha Conde.

Kungiyar ta kuma soki matakan Guinea na daurewa ko kuma hana bangaren adawa ‘yancin fadar albarkacin bakinsu, tana mai cewa kamata ya yi gwamnati ta bayar da cikakkiya damar tofa albarkacin baki da kuma walwalar jama’.

Akwai dai bayanai da ke nuna an tafka arangama tsakanin mabiyan bangaren adawa da jami’an tsaron kasar ta Guinea tun bayan da jagoran adawa ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben bisa alkaluman da jam’iyyarsa ta tattara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.