WTO

Amurka ta ce Ngozi ba ta da kwarewar jagorantar WTO

Tsohuwar ministar kudin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala.
Tsohuwar ministar kudin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala. REUTRS/Nicky Loh

Gwamnatin Amurka ta ce tsohuwar ministan kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala bata da kwarewar da zata iya jagorancin Hukumar Kasuwanci ta Duniya, WTO.

Talla

Amurka wadda ta bayyana adawa da takarar Okonjo-Iweala ranar Laraba, ta ce tana goyan bayan ministar kasuwancin Koriya ta Kudu Yoo Myung-hee saboda ta kware wajen harkokin kasuwanci bayan kwashe shekaru 25 tana aiki a bangaren da ya shafi manufofin kasuwancin.

Sanarwar da Jakadan Kasuwancin Amurka a Hukumar WTO ya gabatar ta ce Myung-hee na da kwarewar da za ta iya jagorancin hukumar a wannan lokaci da ake fuskantar matsalolin kasuwanci da dama tsakanin kasashe da kuma nahiyoyi.

Amurka tace Hukumar Kasuwancin na matukar bukatar garambawul domin sake fasalin ayyukan ta ganin yadda aka kwashe shekaru 25 ba tare da amincewa da sabbin kudaden fito ba da kuma yadda kasashe ke rikici a tsakanin su.

Tuni tsohuwar ministar Najeriya ta samu goyan bayan kasashen ECOWAS da na Turai da kuma wasu kasashe dake Asia wadanda suka kai wakilai 164 dake cikin Hukumar ta WTO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.