Congo

'Yan bindigar ADF sun kashe fararen hula 15 a Jamhuriyyar Congo

Hukumomin kasar sun zargi ADF da silar tserewar daruruwan Fursunoni daga yari.
Hukumomin kasar sun zargi ADF da silar tserewar daruruwan Fursunoni daga yari. Reuters

Rahotanni daga Jamhuriyar Dimokiradiyar congo sun ce 'yan bindigar kungiyar ‘Allied Democratic Forces’ sun hallaka akalla mutane 15 a wani kazamin harin da suka kai kauyen Baeti da ke yankin Beni a Arewacin Kivu.

Talla

Janvier Kasairio, wani jami’i a kungiyar fararen hula ya ce an kai harin ne a daren jiya, kuma bayan kashe mutane an kona gidaje da dama.

Kungiyar ADF wadda aka kafa a shekarar 1990 a Uganda da ake danganta ta da 'yan tawaye, na daga cikin kungiyoyi sama da 100 da ke kai hare-hare a kasar Congo, kuma ana zargin ta da kashe mutane akalla 600 tun bayan kaddamar da sabbin hare hare daga watan Nuwambar bara.

A ranar 21 ga watan Octoba, 'yan Sanda sun zargi kungiyar ADFG da kai harin da ya yi sanadiyyar tserewar daruruwan fursinoni a gidan yarin Beni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.