Mali

An yanke wa 'yan ta'adda 2 da suka halaka turawa hukuncin kisa a Mali

Sabon shugaban wucin gadi na Mali Bah Ndaw da mataimakinsa KanarAssimi Goita a Bamako, Mali.
Sabon shugaban wucin gadi na Mali Bah Ndaw da mataimakinsa KanarAssimi Goita a Bamako, Mali. http://joko.hausa.rfi.fr/sites/hausa.filesrfi/imagecache/REUTERS

Kotu a Mali ta yanke wa wasu mayakan masu ikirarin jihadi 2 hukuncin kisa bayan kama su da hannu a kisan sama da mutane 24 a hare haren da suka kai wa turawa a shekarar 2015.

Talla

Hare haren masu cike da mamaki na daga cikin wadanda aka kai wuraren shakatawa da kuma gidajen cin abinci a Mali, Inda turawan suke, wuraren da tun a shekarar 2012, kazamin rikicin 'yan ta'adda ya shafa.

Tuni dai kotu ta yanke wa Fawaz Ould Ahmed dan asalin Kasar Mauritania da aka fi sani da Ibrahim 10, da abokinsa dan Mali Sadou Chaka hukuncin kisa, bayan shafe tsawon Kwanaki 2 ana zaman shari'ar.

Da soma shari'ar dai Ould Ahmed ya shaida  wa kotu cewar lallai ya Kai hari a wani gidan rawa dake birnin Bamako, inda ya kashe mutane 5 a matsayin martani ga zanen hoton Annabi Mohammad SAW da mujallar Charlie Hebdo, mallakin Faransa tayi. Kana yace basu yi nadama ba, hasali ma suna alfahari da abinda suka aikata.

Kazalika akwai Abdramane Maiga dan Kasar ta Mali, ya kasance na 3 da da hukuncin kisan ya hau kansa, toh saidai bai halarci zaman shari'ar ba.

Ko a shekarar 2015 Wani barfaranshe, da Wani dan Belgium da kuma wasu yan Mali 3 sun gamu da ajalinsu bayan da wasu mayaka suka buda wa wani gidan cin abinci da ke Bamako, mai dauke da turawa wuta, tare da watsa musu barkonun tsohuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.