Najeriya

Sojoji sun fafata da 'yan bindiga a Zamfara

Wasu yan bindiga dauke da makamai a jihar Zamfara
Wasu yan bindiga dauke da makamai a jihar Zamfara REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

A Najeriya an samu arangama tsakanin sojoji da yan bindiga barayin shanu a Gidan Goga dake Jihar Zamfara, kuma an samu rasa rayuka da dama.

Talla

Bayanana dake fitowa daga Yankin sun ce Yan bindiga haye akan Babura dauke da makamai sun kai hari ne jiya da rana, abinda ya sa aka shaidawa sojoji wadanda suka kaiwa mutanen garin dauki, daidai lokacin da Yan bindigar ke kokarin kora dabbobin jama’a, inda akayi ta artabu.Ya zuwa yanzu dai babu adadin mutanen da suka jikkata a harin.

Ko a farkon watan nan na Oktoba,wasu yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a kauyen Tungar kwana na karamar hukumar Talatar Mafara a jihar ta Zamfara tare da kashe akalla mutane 22 lokaci guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.