Kungiyar Turai ta yi Allah wadai da harin da aka kai Faransa
Wallafawa ranar:
Shugabannin Kungiyar Turai sun yi Allah wadai da harin da aka kai Faransa, inda suka bukaci kasashen duniya da su yi aiki tare wajen tattaunawa da fahimtar a tsakanin al’umma da kuma addinai maimakon rarrabuwar kawuna.
Sanarwar da shugaban Majalisar Turai Charles Michel ya gabatar tace shugabannin kasashen Turan 27 sun bayyana goyan bayan su ga Faransa amma kuma sun ki cewa komai dangane da cece kucen da ya biyo bayan zanen batuncin da ake yiwa addinin Islama.
Sanarwar tace su shugabannin Turai sun kadu da harin na Faransa, inda suka bukaci shugabannin kasashen duniya da su hada kai wajen tattaunawa da fahimtar juna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu