Kotun Kenya tayi wa matasa biyu daurin shekaru 33 saboda taimakawa ta'addanci

Mayakan Al-Shebab a kasar Somaliya
Mayakan Al-Shebab a kasar Somaliya

Wata babar Kotu a Nairobin kasar Kenya ta yankewa wasu da suka taba kai hari a wani shagon sayar da kaya hukuncin daurin shekaru 33.

Talla

Mutane biyun da kotun ta yankewa hukuncin suna cikin wadanda ake zargi da kai hari a wani baban shagon sayar da kaya dake birnin Nairobin kasar a shekarar 2013, harin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 67.

Kotun ta same su da hannu dumu dumu da laifin taimakama mayakan kungiyar Alshabab ta kasar Somalia da suka dau alhakin kai harin, a wancan lokaci,inda tayi musu hukuncin daurin shekaru 33 kowannen su, to sai dai maharani da aka shigo dasu dakin shara'ar fuskokinsu a  rufe, sun roki alkali da ya yi musu sassauci domin kuwa sun shafe shekaru bakwai a tsare, kuma sunada iyalai da ya kamata ace suna kulawa dasu.

An bayana harin a matsayin hari mafi muni a kasar Kenya cikin shekaru 15, bayan harin da aka kai ofishin jekadancin Amurka wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 213,harin da aka watsa kai tsaye ta gidanjen TV tsawon kwanaki hudu ana artabu da jami’an tsaron kasar kamin samun nasara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.